Makomar yammacin Sahara | Labarai | DW | 12.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar yammacin Sahara

Moroko da kungiyar yan polisario masu neman yancin kai sun cimma amincewa da cigaba da tattaunawa dagane da makomar yankin yammacin sahara,sai kowanensu na nan kann kaidoji daya gindaya,a zagaye na biyun tattaunawarsu da wakilan mdd.Wakilin kungiyar Polisario dake mdd Ahmed Boukhari ,ya shaidawa manema labaru cewa ,mdd ta kaddamar da wasu kudurori guda biyu ,wanda keda nufin kawo karshen wannan takaddama daya dauke shekaru 32 ,akan wannan yanki na arewacin Afrika,sai dai yace Moroko tayi watsi dasu.Na farkon injishi,ya shafi harkokin tono dukkan nakiyoyin karkashen kasa a yankin na yammacin sahara,ayayinda batu na biyu ya shafi yancin biladama.Boukhari yace,baki dayan mahalarta taron a biornin New York basu ji dadin ,rashin amincewar Moroko kann wadannan batutuwa ba.