Makomar taron G8 | Siyasa | DW | 06.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makomar taron G8

Ba a hangen cewar taron kasashen G8 zai haifar da wani sakamakon kirki akan maganar yanayi

Zanga-zangar adawa a taron G8

Zanga-zangar adawa a taron G8

Idan an ajiye maganar zanga-zanga da tashe-tashin hankulan da aka sha fama da su daga bangaren wasu masu neman yin amfani da adawar masu kyamar kusantar tattalin arzikin da ake dada samu tsakanin sassan duniya daban-daban domin ta da zaune tsaye, ainifin nasarar taron kolin ya danganta ne da daidaituwa ko kuma sabanin da za a fuskanta akan manufar kare makomar yanayi tsakanin mahalarta taron. Da farkon fari dai shugabar gwamnatin ta Jamus ta saka dogon buri game da samun ci gaba a zauren taron bisa wasu dalilai kwarara. Domin kuwa maganar dimamar yanayin da ake samu sakamakon wasu abubuwa masu illa ga makomar yanayi da kasashe masu ci gaban masana’antu da kuma masu matsakaicin ci gaba ke fitarwa zuwa sararin samaniya dangane da aiwatar da makamashi fiye da kima, matsala ce da ta shafi kowa-da-kowa a doron duniyar nan tamu. Wato dai maganar ta shafi makomar rayuwar dan-Adam ne baki daya. Amma tun kafin a fara taron aka gano cewar ba za a samu ci gaban da ake bukata a wannan manufa ba. Shugaba Goerge W. Bush yayi wa shirin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zagon kasa, inda ya gabatar da tasa shawarar wadda tayi daura da ta Angela Merkel, amma tayi daidai da bukatun kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu. Kasashen China da Indiya da Brazil da sauran kasashe masu tasowa zasu ba da hadin kai ga Amurka domin hana ruwa gudu ga manufar kare makomar yanayin duniyar. Su dai kasashe masu tasowa suna da dalilansu domin kuwa kayyade yawan sinadari mai haddasa dimamar yanayi da suke fitarwa zuwa sararin samaniya na ma’anar kashe makudan kudi domin sauya hanyoyinsu na samun makamashi, lamarin da ya daya bangaren ke nufin cikas ga bunkasar tattalin arzikinsu. A sakamakon haka wadannan kasashe ke cewar faufau ba zasu yarda da haka ba, saboda sun gaji da zama ‘yan rakiya ga kasashe masu ci gaban masana’antu na Turai da Japan da kuma arewacin Amurka. Bugu da kari kuma su kansu kasashe masu ci gaban masana’antu basu kaunar canza tsare-tsarensu na samun makamashi a yayinda suke fafutukar shawo kan kasashe masu tasowa da su yi haka. A saboda haka a zauren taron kolin na G8 babu wata takamaimiyar daidaituwar da za a cimma akan wannan batu. Amma dangane da taimakon ga nahiyar Afurka kuwa mai yiwuwa a samu gagarumin ci gaba, musamman a bangaren bunkasa yawan taimakon raya kasa, inda Jamus ke da niyyar yin karin Euro miliyan 750 tun daga shekara mai zuwa, domin yakar cutar AIDS da kyautata manufofin ilimi da makomar jin dadin rayuwar al’uma a wannan nahiya, saboda ta haka ne kawai za a dakatar da tuttudowar ‘yan gudun hijirar Afrukan zuwa nahiyar Turai.