Makomar shariár Hissene Habre | Labarai | DW | 25.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar shariár Hissene Habre

Kotun daukaka kara ta kasar Senegal ta baiyana cewa ba ta da hurumi na zartar da hukunci akan bukatar da kasar Belgium ta gabatar ta neman a tasa mata keyar tsohon shugaban kasar Chad Hissene Habre wanda ake nema ruwa a jallo domin amsa tuhuma a game da tabargazar da aka tafka a zamanin mulkin sa. Babu dai tabbaci a game da ko wace hukuma ce kuma zata sake daukaka karar. Takardar sammacin da kasar Belgium din ta bayar ya zargi Hissene Habre da laifin azabtarwa da kisan kare dangi wanda yan sandan kasar suka aikata a zamanin mulkin sa, a tsakanin shekarun 1982 zuwa 1990. Hissene Habre mai shekaru 63 da haihuwa ya shafe tsawon shekaru 15 yana gudun hijira a kasar Senegal. A makon da ya gabata ne aka kama shi a birnin Dakar domin tasa keyar sa zuwa gida, to sai dai lauyoyin sun baiyana cewa Habre ba shi da masaniya a game da kisa ko azabtarwa da cin zarafi da yan sanda suka yiwa mutanen da ake tsare da su a gidan yari a zamanin mulkin sa.