1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariá kan Guantanamo

Abdullahi T. BalaJune 13, 2008

Yan gidan yarin Guantanamo na iya ƙalubalantar cigaba da tsare su ba tare da shariá ba.

https://p.dw.com/p/EJRq
Babbar kotun ƙolin AmirkaHoto: AP

Kotun ƙolin Amirka ta zartar da hukunci cewa mutanen da ake tsare da su a sansanin Gwale-gwale na Guantanamo suna da damar shigar da ƙara a kotun tarayya ta Amirka domin ƙalubalantar cigaba da tsare su da ake sansanin na Guantanamo.

A karon farko shugaban Amirka George W Bush ya gaza samun goyon bayan alƙalan kotun ƙolin Amirka a game da ikon cigaba da tsare mutanen da Amirkan ke zargi da ayyukan taáddanci a sansanin Gwale-gwale na Guantanamo ba tare da tuhuma ba.

Kotun ta ce mutanen waɗanda ake tsare da su a sansanin na Guantanamo suna da dama bisa hurumin doka su ƙalubalanci cigaba da tsare su a sansanin ba tare da tuhuma ba, kotun ta ƙara da cewa ba daidai bane a cigaba da riƙe mutanen ba tare da an gabatar da su gaban shariá ba kuma bai dace ba a gurfanar da su gaban kotun soji ba.


Wasu daga cikin mutanen 270 da ake tsare da su, sun shafe fiye da shekaru shida a sansanin na Guantanamo. An gurfanar da 80 daga cikin su a gaban kotun soji wadda yan Majalisar dokoki masu rinjaye na jamýar republican suka amince da kafuwar sa.


Kotun sojin da ya zuwa wannan lokaci ta sami sukunin sauraron gabatar da ƙararraki ne kawai. A yan kwanakin nan ne aka saurari ƙararrakin mutum biyar daga cikin waɗanda ake tuhuma da harin nan na 11 ga watan Satumbar shekara ta 2001.


A sakamakon wannan hukunci na kotun ƙoli dukkanin mutanen suna iya shigar da ƙara a gaban kotun farar hula domin neman a sake su.


Da yake bayani a birnin Rome game da hukuncin kotun, shugaban Amirka George W Bush yace ko da yake yana adawa da wannan hukunci, duk da haka zai rungumi abin da shariá ta zartar. Yace kotun ita kanta ta sami rarrabuwar kawuna, yace ya yarda da raáyin waɗanda suke adawa da wannan hukunci, domin sun yi hakan ne bisa damuwar da suke da ita ga shaánin tsaron ƙasar Amirka.


Abin tambaya shine shin ko akwai yiwuwar yan majalisar dokoki na republican za su buƙaci yin gyara ga ƙudirin dokar da zata bada damar cigaba da tsare mutanen ba tare da tuhuma ba ? Jeff Toobin wani masanin shariá yace a yanzu dai kam lokaci ya ƙurewa yan majalisar dama shi kan shugaban Amirka George Bush. Yace idan aka yi laákari da yadda alámura ke tafiyar hawaniya a Guantanamo, babu ko tantama makomar sansanin baya ga hannun Bush amma ga wanda zai gaje shi.


Batun rufe sansanin na Guantanamo abu ne dake jiran lokaci, hatta ga John McCain ɗan mazan jiya yana da wannan raáyi. McCain yace labudda zaá rufe wannan sansani, amma kuma zaá cigaba da tsare mutanen da ake tuhuma a barikin sojoji dake jihar Kansas.


To amma ga Barrack Obama na jamíyar Democrats raáyin su ya banbanta. Bama kawai yana sukar lamirin sansanin na Guantanamo bane kaɗai yana ma kuma adawa da yiwa mutanen shariá a kotunan soji. Obama yace idan ya kasance shugaban ƙasa zai rufe wannan sansani ya kuma yi watsi da tsarin kotun sojin yana mai cewa zai yi aiki ne da ƙudirin Geneva na Majalisar Ɗinkin Duniya.


Nan da yan kwanaki masu zuwa alƙalan kotun ƙolin za su hallara domin fayyace yadda zaá aiwatar da wannan gagarumin aiki kuma mai rikitarwa.