Makomar Rikicin Yankin Gabas Ta Tsakiya Bayan Yassir Arafat | Siyasa | DW | 10.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makomar Rikicin Yankin Gabas Ta Tsakiya Bayan Yassir Arafat

Akasarin al'umar Isra'ila ba su da sikankancewa cewar za a samu wani ci gaba a shawarwarin Yankin Gabas ta Tsakiya a karkashin sabbin shuagabannin da za a nada bayan mutuwar Malam Yassir Arafat

Akasarin al’umar Isra’ila na tababa a game da cewar za a samu wata sabuwar kafa ta shiga shawarwarin sulhu mai ma’ana da sabbin shuagabannin Palasdinawan da za a nada bayan rasuwar Malam Yassir Arafat. Sakamakon binciken da jami’ar Tel Aviv ta gudanar yayi nuni da cewar kimanin kashi 58% na Yahudawa da kashi 52% na Larabawan Isra’ila ke tattare da imanin cewar babu wani ci gaban da za a samu na gudanar da shawarwarin sulhu masu ma’ana bayan nadin sabbin shuagabanni a fadar mulkin Palasdinawa ta Ramallah. Kimanin kashi biyu bisa uku na Isra’ilawa ke tattare da imanin cewar har yau Palasdinawa basu gamsu da hakkin wanzuwar Isra’ila a zukatansu ba. Kuma da zarar wata dama ta samu a garesu ba zasu yi wata-wata ba wajen murkushe kasar Isra’ilar, kamar yadda sakamakon binciken, wanda jaridar Haaretz ta buga a jiya talata, ya nunar. Duka-duka kashi 13% na al’umar Isra’ila ne ke da akasin wannan ra’ayi. Su dai Isra’ilawa sun dade suna kyamar manufofin Malam Arafat tare da fatali da rawa ta tarihin da ya taka a game da yankin Gabas ta Tsakiya da manufofin Palasdinawa. Kimanin kashi 80% na Isra’ilawa ke wa Yassir Arafat kallon dan-ta’adda, a yayinda kashi 5% ne kacal suka dauke shi tamkar wani shugaba ma’abuci dattaku. Dalili kuwa shi ne sikankancewar da suka yi cewar shugaban na Palasdinawa na da kakkarfan angizo, musamman ma akan ‚yan tsageran dake da zazzafan ra’ayi a yankunan Palasdinawa masu ikon cin gashin kansu. Wato dai a takaice suna dora masa alhakin hare-haren ta’addanci da na kunar bakin waken da ake kaiwa kan farar fular Isra’ila. To sai dai kuma idan an yi bitar maganar a bangarori na siyasar jam’iyyu za a ga banbance-banbancen ra’ayi a tsakanin Isra’ilawan. Domin kuwa a bangaren magoya bayan jam’iyyar Likud ta masu zazzafar akidar Yahudancin dake mulki a Isra’ilar, kusan dukkansu na la’antar Arafat a matsayin wani hatsabibin mutum, a yayinda a bangaren magoya-bayan jam’iyyar Labour mai sassaucin manufofin siyasa, duka-duka kashi 50% ne daga cikinsu ke dauke da ra’ayin cewar Arafat dan ta’adda ne. Isra’ilawan na takaicin ba wa Arafat damar komawa gida da aka yi a karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo da aka cimma a shekara ta 1994, daga zaman hijirar da yake yi a Tunesiya. A dai halin da ake ciki yanzu gwamnatin Sharon tana sara tare da duban bakin gatarinta, saboda gudun furta wani abin da ka shafa wa daya daga cikin magadan Arafat din kashin kaza. A takaice akasarin al’umar Isra’ila ba su da kwarin guiwa a game da abin da zai biyo bayan Yassir Arafat, bisa sabanin ikirarin da Amurka da kawayenta na nahiyar Turai ke yi na cewar mutuwar shugaban Palasdinawa ka iya ba wa shawarwarin zaman lafiyar Yankin Gabas ta Tsakiya wani sabon jini akan manufa.