Makomar Palestinawa a rikicin Gabas ta Tsakiya | Zamantakewa | DW | 05.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Makomar Palestinawa a rikicin Gabas ta Tsakiya

Hukumar Palestinu ta bayyana shakku game da cimma nasara warware rikicin Gabas ta Tsakiya

default

M.Abbas da B.Obama na ganawa game da rikicin Gabas ta Tsakiya

Tun hawan shugaban ƙasar Amirka Barack Obama kan karagar mulki, ya bayyana aniyar shawo kan rikicin tsakanin Israi´la da Palestinu da shinfiɗa  zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Gabas ta tsakiya, to sai dai har yanzu Palestinuwa ba su gani ba ƙass.

A lokacin yaƙin neman zaɓe Barack Obama ya bayyana burinsa na warware wannan rikici da ya ƙi ya ƙi cenyewa ta hanyar tattanawa.

Bayan yayi nasara lashe zaɓen, jim kaɗan bayan hawan sa kan karagar mulkin White House, ya naɗa George Mitchel a matsayin wakili na wakili na mussamman a yankin Gabas ta Tsakiya.A lokacin duniya ta yaba masa tare da cewar da alamun da gaske ya ke yi saɓanin  magabacinsa Georges Bush.

To sai dai ya zuwa wannan lokaci har yanzu dai a nan gidan jiya noman goje kamar yadda shi da kansa shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas ya bayyana:

"Mu na buƙatar rayuwa cikin walwala da zaman lafiya.Fiye da shekaru 62 mu na fama cikin uƙuba.Ina fata wata rana ɗiya da jikokina da kama kunnai su samu rayuwa kyakkayawa, saɓanin yadda mu ka rayu a wannan yanki, to amma ta la´akari da yadda al´ummura ke gudana na rumtse idoiban ga kyan makamta ba."

Har yanzu dai shugaban na Amurika ya ce ba za shi ƙasa a gwiwa ba, wajen faɗi ka tashin neman zaman lafiya.Ya bayyanawa ´yan jarida hakan a wata ganawa da yayi bayan bayan tare da Sarki Abdellah na Saudiyya:

"Mun tatana game da batun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, mussamman yadda za a girka ƙasashe biyu wato Palestinu da Isra´ila wanda za su maƙwabtaka da juna irin ta girma da arziki cikin kwanciyar hankali da lumana."

Domin cimma wannan buri ne ma shugaban Amurika ya sake tura George Mitchel a yankin domin tattanawa da ɓangarori daban-daban da lamarin ya shafa.

Sannan  a wani a wani abu da za iya dangatawa da ɗan cigaba, an gana jiya Litinin tsakanin Firaministan Palestinu Salam Fayyad da ministan tsaron Isara´ila Ehud Barack a matsayin share fage ga tattanawar da zata haɗa Barack Obama da Firaminstan  Isra´ila Benjamin Natenyahu a birnin Washington.

Sai dai wata matsala da ake tunanin zata hana ruwa gudu a yunƙurin warware wannan taƙƙadama, itace rikici tsakanin Hamas da Fatah, wanda sanadiyar hakan Palestinu ta kasance rabe ɓangarori biyu masu gaba da juna

Mawwallafi: Yahouza Sadisou Madobi Edita: Mohamed Nasiru Awal