Makomar manufofin Jamus a Afghanistan | Siyasa | DW | 05.10.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makomar manufofin Jamus a Afghanistan

Muhimmin batun da zai fi ɗaukar hankalin sabuwar gwamnatin da zaá kafa a Jamus shine tsawaita aikin sojojin ƙasar a Afghanistan. Shin yaya manufar Jamus zata kasance a karkashin gwamnatin haɗakar ta CDU da FDP ?

default

Sojojin Jamus a Afghjanistan.

A kwanakin baya ne wata kafar yaɗa labaru a Jamus ta ruwaito cewa zaá ƙara yawan dakarun ƙasar a Afghanistan izuwa sojoji 7,000, to amma tuni maáikatar tsaro ta yi watsi da wannan rahoton da cewa jita-jita ne kawai. A saboda haka dai babu wani sauyin alƙibla a dangane da manufofin Jamus a Afghanistan.

A yanzu haka dai Jamus na da sojoji 4,200 da aka girke a arewacin Afghanistan ƙarƙashin rundunar ISAF. Babu shakka sabuwar gwamnatin CDU da FDP zata ƙara waádin sojojin da shekara guda a Afghanistan inda ake sa ran majalisar dokoki zata amince da wannan ƙudiri.

Shugabar gwamnati Angela Merkel tace aikin dakarun ba abu ne da zaá yi watsi da shi ba. " Tace Suna bada gudunmawa ta fannin tsaron ƙasa da ƙasa da kuma samar da zaman lafiya, tare da kare rayuwar alúmar kasarmu daga munanan ayyukan yan taádda na ƙasa da ƙasa. Wannan shine manufar aikin su kuma har yau bamu chanza ba".

Ita ma Jamíyar FDP sabuwar abokiyar ƙawancen tana da irin wannan raáyi kamar yadda shugabanta Guido Westerwelle wanda bisa ga dukkan alamu shine zai zama sabon Ministan harkokin wajen Jamus ya faɗa. " Ba zaá iya gina Asibiti ko rijiya a Afghanistan ba, da dukkan wani aiki na jin kai ba, da da don an girke sojojin rundunar Bundeswehr a Afghnistan ɗin ba, wadanda suka sadaukar da rayukan su don gudanar da wannan gagarumin aiki na sake gina ƙasar.

A hannu guda dai yan Jamíyar ta FDP sun nuna rashin gamsuwa kan yadda aikin bada horo ga yan sandan Afghanistan yake tafiyar hawainiya, baá tura ƙwararun jamián yan sanda dana soji da suka dace don gudanar da wannan aiki ba.

A cewar shugabar gwamnati Angela Merkel zaá cike wannan gibi ne a yayin babban taro kan Afghanistan, ta kuma tattauna wannan manufa da ƙasashen Faransa da Britaniya inda suke fatan gudanar da taron a wannan shekarar.

" Baki ɗaya dai babban manufar taron shine samar da ƙwararun jamián horaswa don bada horo mai inganci ga jamián tsaron Afghanistan tare kuma da tsara jadawalin lokacin da zaá bada wannan horo.

Merkel ta ƙara da cewa duk wani horo da zaá baiwa yan sanda da sojojin ba zai yi wani amfani ba saboda ƙarancin albashi mai tsoka daga gwamnatin Karzai wadda farin jininta ke raguwa sakamakon magudin zaɓe da ake zarginta da tafkawa.

Kawo yanzu dai gwamnatin Jamus na yin kafa-kafa ga tura sojoji saboda har yanzu Amurka bata tsayar da shawara ba game da tura ƙarin sojoji a Afghanistan, bayan da babban kwamnada Janar Stanley McChrystal ya yi kira da a ƙara yawan dakarun NATO a ƙasar.

Mawallafa: Nina Werkhäuser/ Abdullahi Tanko Bala

Edita: Mohammad Awal