MAKOMAN KASUWANCIN KAYAYYAKIN ALBARKATUN NOMA A TURAI. | Siyasa | DW | 19.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MAKOMAN KASUWANCIN KAYAYYAKIN ALBARKATUN NOMA A TURAI.

Kasashen da ke cikin Kungiyar Ciniki Ta Duniya dai, sun san cewa ba za su iya kauce wa nauyin da ya rataya a wuyarsu, na warware rikicin da ya janyo rashin jituwarsu a taron da suka yi a birnin Cancun na kasar Mexico a shekarar bara ba. Kafin dai a sami wani ci gaba, sai sun cim ma wata madafa, wadda kowa zai iya amincewa da ita. A halin yanzu dai, duk kasashen na fatar cewa, za a iya shawo kan matsalolin nan ba da dadewa ba. kasashen da ba su cikin kungiyar ma, kamar Rasha, sun nuna sha'awarsu ta ganin cewa an sami ci gaba a tattaunawar.

Stuart Harbinson, shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin noma na kungiyar. Game kokarin da ake yi na cim ma daidaito a shawarwarin kungiyar da kuma inganta harkokin cinikayya a kasuwannin duniya dai, ya bayyana cewa:-

"Kungiyar WTO dai za ta iya bude wa kasashe masu tasowa wata kofa ta bunkasa cinikayyarsu. Amma bai kamata mu yi wa wannan lamarin wani kallo karkashin jigon Arewa da Kudu ba. Duk masu fada a ji a tattaunawarmu dai, sun san cewa an sami jituwa a kan batutuwa daban-daban da suka shafi matsayin kasashe masu arzikin masana'antu da kasashe masu tasowa."

A nan Jamus kuma, ministan noma ta tarayya, Renate Künast, ta yabi yunkurin da kasashe masu tasowa da kungiyoyin sa kai ke yi, wajen kare maslaharsu, a yanzu, fiye da da. A nata ganin dai, lokaci ya zo da ya kamata a tafiyad da harkokin kungiyar Ciniki Ta Duniyar, ta hanyar dimukradiyya:-

"Na yi imanin cewa, idan aka sami adalci a harkokin cinikayyar duniya, to ba za a sake maimaita kurakuran da aka yi a kasashe mawadata, a kasashe masu tasowa na kudancin duniya ba. Sabili da haka ne kuwa, nake karfafa cewa, kamata ya yi, a tattauna kome daga kare hakkin masu amfani da kayayyakin noma, zuwa ga kare kewayen bil'adama da dai sauran duk wasu jigogin da ke da muhimmanci wajen cim ma daidaito a wannan harkar."

To ministan dai na da kyakyawar manufa. Amma fa aiwatad da ita a nan Turai ma, ba karamin aiki ba ne. Har ila yau dai, ra'ayoyi sun bambanta kan yadda za a tsara hanyoyin kiwon dabbobi mafi inganci, ta yin la'akari da kare lafiyar jama'a. A halin yanzu dai, abin da aka cim ma kawai ne, tabbatar da cewa, sabbin kasashe 10 nan da za su shiogo cikin Kungiyar Hadin Kan Turai, a cikin watan Mayu mai zuwa, sun cika ka'idojin tafiyad da harkokin noma da ake amfani da su a tsoffin kasashen kungiyar.

Amma ga su sabbin kasashen kungiyar, ba cika ka'idojin ne abin da ya fi ci musu tuwo a kwarya ba. Suna son su san yadda harkokin cinikayyar da suke yi da kasashen gabashin Turai kamarsu Rasha za su kasance ne bayan sun zamo cikakkun mambobin kungiyar. Kamar yadda ministan noma na kasar Sloveniya ya bayyanar:-

"Ina fatar cewa, za a kuma yi la'akari da harkokin cinikayyar da muke yi da kasashen Rasha, da Ukraine, da kasar Bellruss da sauran kasashen gabashin Turai. Muna dai kyautata zaton cewa, za a bai wa kayayyakin nomanmu darajar da ta zo daidai da na sauran tsoffin kasashen kungiyar." Sauran kasashen gabashin Turan, kamarsu Rasha dai na fargabar cewa, idan aka fadada kungiyar a cikin watan Mayu ta kunshi mambobi 25, za su huskanci wata cikas a harkokin cinikayyar albarkatun nomansu. Ministan noman Rashan, Alexej Gordejew ya bayyana damuwarsa ga irin rashin adalcin da ake samu a Kungiyar Ciniki Ta Duniya a halin yanzu, duk da cewa, kasarsa ba ta cikin kungiyar:-

"A kungiyar WTO din, babu wata kyakyawar hanya ta tattaunawa. Abin damuwa a nan dai shi ne, nan gaba, masu wadatan ne za su kara arziki, sa'annan matalautan kuma su kara talaucewa. Bai kuwa kamata a yi hakan ba. Bai kamata kasashe mawadatan su dauki matalautan kamar wan i abin ganima ba."

Babban kwamishinan noma na Kungiyar Taryyar Turai Franz Fischer, ya musanta wannan fargabar da kasashe kamarsu Rashan ke yi. Ya dai bayyana cewa, a halin yanzu an kawo karshen yakin cacar baka da na cinikayya. Gurin da kungiyarsa ta sanya a gaba ne, kago wani yanki na kulla huldodin abokantaka.
 • Kwanan wata 19.01.2004
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmT
 • Kwanan wata 19.01.2004
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmT