makamin linzami mai dogon zango | Labarai | DW | 19.06.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

makamin linzami mai dogon zango

Kasar Koriya ta arewa na dada fuskantar matsin lamban kasashen duniya,bias rade radin cewa tana shirin kaddamar da makamin linzaminta,mai nisan zango.Tun a shekarata 1999 nedai,kasar ta daina kaddamar da makamai masu nisan zango.Idan ta cimma kaddamar da wannan makami na linzamin,ba karamin damuwa zai haifar ba wa kasashen dake makwabtaka da ita,kana da Amurka a daya hannun.Tun da akwai has ashen cewa wannan makami da take shirin kaddamarwa,zata iya harba shi zuwa Amurka.Akan hakane jakadan Amurka a mdd John Bolton,yace kasarsa na tuntuban sauran wakilan komitin sulhu ,adangane da matakan da zaa dauka kan Koriya ta arewa,idan harta kaddamar da wannan makamin linzami mai nisan zango.A shekara ta 1998 nedai Kasar ta koriya ta kaddamar da irin wannan makami ,wanda ta harba ta kan arewacin Japan,makamin daya fada tekun pacific.

 • Kwanan wata 19.06.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6Y
 • Kwanan wata 19.06.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6Y