1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Makamashin nukiliya a Afirka

Gina tashoshin makamashin nukiliya a matsayin sabuwar hanyar magance matsalar wutar lantarki a Afirka.

default

Yuƙurin gina tashoshin makamashin nukiliya a Afirka

Kusan baki ɗaya, ƙasashen Afirka na fama da matsalolin wutar lantarki, abinda ke jawo babban koma baya ta fannin cigaban kamfanoni da masana´antu.Masana sun  gano cewar magance matsalar wutar lantarki a Afrika, na matsayin hanyar warke matsalar fatara da talauci da nahiyar ke fama da su.

Ƙiddidigar Hukumar Makamashi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewar kashi 70 cikin ɗari a al´ummomin dake raye a Afrika kudancin Sahara basu da wutar lantarki.Saboda haka,da dama daga gwamnatocin ƙasashen suka himmantu domin ɓullo da wata sabuwar husa´ar wadatar da jama´a da hasken wutar lantarki, ta hanyar makamashin nukiliya.To saidai ƙalubale a nan shine makamashin nukiliya na da haɗarin gaske, sannan aiki ne dake buƙatar tsabar kuɗi masu yawan, wanda akasari ƙasashen ba su da shi.

A halin yanzu ko wace ƙasar Afirka na nuna shawar mallakar makashin nukilya domin samun wadata ta fannin wutar lantarki, to saidai a cewar Zephirin Diabré shugaban sashen Afrika da Gabas ta Tsakiya a kamfaninn sarrafa makashin nukiliya na ƙasar Fransa wato AREVA, samar da makashin nukiliya  a Afrika abu ne dake yiwuwa to amma ya gitta sharruɗa kamar haka:

" Duk ƙasar dake buƙatar samun makamashin nukiliya dole sai ta girka tubalin tushe na gari ta fannin dokoki, sannan mataki na biyu ta samar da jami´ai ƙurraru wanda zasu ƙaddamar da tsarin su kuma tafiyar da shi ta hanyar da ya dace.Hakan zai taimaka a tabbatar da makamashin nukiliya mai inganci."

Haƙiƙa ga  AREVA, buri ne da Afrika ke iya cimma, domin kamfanin ya ƙurre ta fannin husa´ar makamashin nukiliya, kuma ya na samun ɗumbin makamashin Uranium dage Jamhuriysa Nijar.Saboda haka ne ma,Faransa ta kasance ƙasar farko aTurai da tafi amfani da irin wannan husa´ar makashi, to saidai game da ƙasashen Afrika ba a nan gizo ke saƙa ba, inji Anne -Sophie Corbeau ta hukumar makamashin ƙasa da ƙasa dake birnin Paris na ƙasar Faransa:

"Aiki ne mai matuƙar tsada.Ayar tambaya itace shin anya kuwa gwamnatocin ƙasashen Afirka zasu iya zuba kuɗin da zasu ɗauki ɗawainiyar wannan aiki ? Su dai ƙasashen na Afirka ba su da ƙurewa ta wannan fanni, cilas sai sun ɗauko hayar ƙurraru da kuma husa´a da kayan aiki daga ƙetare."

Tuni dai wasu ƙasashen Afrika duk da ƙarancin tatalin arzikin, sun bayyana aniyar mallakar tashoshin makamashin nukiliya.

Ministan makamashi na Senegal, ya ce ƙasar zata mallakai irin wannan tasha nan da shekara ta 2020,itama Majalisar Dokokin ƙasar Uganda ta rattaba hannu akan dokar samar da tashar makashin nukiliya. A halin da ke ciki kuma,ana tafka mahaura a kafofin sadarwa  Keniya  game da wannan batu.Amma a cewar Horst Blume wani bajamushe dake fafatukar yaƙi da girka tashoshin samar da makamashin nukiliya ya gargaɗi ƙasashen Afirka game da illolin wannan cibiyoyi.Yayi masu tuni da bila´in da ya faru a tashar nukiliya ta Tschernobyl ta ƙasar Ukraine a shekara 1986, inda dubunan jama´a suka rasa rayuka sanadiyar fashewar wata rundunar iskan gas.

Mawwalafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Mohammad Nasiru Awal