1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majami’ar Dom ta Birnin Kolon

Abba BashirSeptember 5, 2005

Tarihin Majami’ar Dom ta Birnin Kolon

https://p.dw.com/p/BwXQ
Majami'ar Dom
Majami'ar DomHoto: AP

Masu sauraronmu assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta hadin gwiwa ce, daga Malam Attahiru Zakari,mai akwatin gidan waya 4532 Jihar Sokoton Tarayyar Najeriya. Yace don Allah, ina so ku ba ni tarihin Majami’ar ta Birnin Kolon na Kasar Jamus.

Amsa: Majami’ar Dom dai ta na nan a gefen babbar kasuwar Birnin Kolon da kuma babbar tashar jiragen kasa da ke Birnin, kuma ta na daya daga cikin abubuwan tarihi da masu yawon shakatawa suke kawo ziyara dominsu.

Majami’ar dai, Majami’a ce ta mabiya darikar katolika, wadda aka fara gininta tun cikin shekarar 1248, amma ba’a kammala aikin ba sai a cikin shekara ta 1880.

An gina ta ne akan harabar wata Majami’ar da aka gina a cikin karni na shida. Kuma an gina ta ne don tunawa da wasu sarakuna uku wadanda suka ziyarci Yesu kiristi a lokacin da ya ke karami.

Wannan Majami’a ta kunshi wani guri da masana tarihi ke kyautata zaton makwantan wadannan sarakuna ne. Wani mutum da ake kira da suna Nikolas Nabadung ne ya tsara wannan wuri sannan aka fara gininsa a shekarar 1180 ,aka kuma kammala a shekara ta 1230.

Hasumiyoyinta wadanda kowacce daya tsawonta yakai kafa 156 an fara gininsu ne a cikin shekara ta 1310 amma ba’a kammala ba sai a cikin shekara ta 1880.

Sauran abubuwan da majami’ar ta kunsa na tarihi sun hada da mutum-mutumin Mary wanda aka fi sani da suna Malenda – Madona. Anyi wannan mutum-mutumi ne a shekarun 1290.A ciki akwai kyawawan kujerun zama na katako mai kyau, wadanda aka yi tun cincin shekara ta 1320. Har’ila yau majami’ar ta Dom ta kunshi tagogi na gilasai wadanda aka yi su tun cikin karni na goma-sha-hudu.Har’ila yau kuma akwai darduma da wani Bajamushe mai suna Peter Doll Rubens ya saka tun cikin shekara ta 1640.

‘Yan yawon shakatawa daga sassa daban-daban na Duniya da ke kawo ziyara nan kasar Jamus, sukan dangana da wannan majami’a.