Majalisun dokokin Amirka sun amince da kashewa yakin Iraƙi da Afghanistan biliyoyin dala | Labarai | DW | 25.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisun dokokin Amirka sun amince da kashewa yakin Iraƙi da Afghanistan biliyoyin dala

Dukkan majalisun dokokin Amirka biyu sun amince da wani shirin doka wanda ya tanadi kashe kudi biliyoyin dala ga yakin da ake yi a Iraqi da kuma Afghanistan, ba tare da sanya lokacin janye dakarun kamar yadda jam´iyar democrat ta nema ba. Da farko shugaba Bush ya nunar da cewa dole Amirka ta samarwa dakarun ta isassun kudade da kuma kayan aiki da suke bukata don samun nasara kan abokan gaba. Shugaban na Amirka ya fadawa wani taron manema labaru a fadar White House cewa ´yan watanni masu zuwa zasu kasance wani lokaci mai matukar wuya ga dakarun Amirka a Iraqi. Bush ya ce fada zai kazanta bayan an kara yawan dakarun Amirka a Iraqi a tsakiyar watan yuni. A tashe tashen hankulan da suka ki ci suka ki cinyewa a Iraqin an halaka mutane akalla 30 sannan aka jiwa da dama rauni a wani harin bam da aka kai da mota a garin Fallujah.