1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

majalisar Turkiya ta shirya zaben shugaban kasa

August 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuCw

Majalisar dokokin kasar Turkiya ta shirya zaben ministan harkokin waje Abdulahi Gul a matsayin shugaban kasa bayan ya kasa samun isassun kuriu a zabuka biyu na baya da aka gudanar.Ana sa rab Gul zai samu nasara a zagaye na uku na zaben a yau wadda ake bukatar kuriu 276 kadai cikin majalisar mai membobi 550.A makon daya gabat jamiyar dake mulki ta AKP ta gagara samun kashi biyu bisa uku na kuriu da ake bukata a zaben shugaban kasa cikin zagaye biyu na kuriun.Zaben Abdullahi Gul zai zama babban nasara ga jamiyar masu raayin islama ta AKP kan yan jamiyun da basa goyon bayan hada addini da mulki wadanda kuma suka kawo ciksa ga kokarin Gul na darewa kujerar shugaban kasa na watan Afrilu saboda raayin musulunci da yake da shi.Wannan rikici dai ya tilastawa firaminista Racep Tayyib Erdogan gaggauta kiran zabe da jamiyar ta AKP ta samu gagarumin rinjaye cikinsa.