1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Majalisar Turai Ta Nada Shugabanta

A zaman farko da tayi bayan zaben da aka gudanar watan yunin da ya wuce a yau talata majalisar Turai ta nada Josep Borrell domin shugabancinta na tsawon shekaru biyu da rabi

Josep Borrell shugaban majalisar Turai

Josep Borrell shugaban majalisar Turai

Kimanin wakilai 388 daga cikin wakilai 737 na majalisar suka ba wa dan takarar goyan baya sakamakon hadin guiwar da aka samu tsakanin ‚yan mazan-jiya da ‚yan socialists da suka fi rinjaye a majalisar ta Turai dake garin Strassburg. Wakilan jam’iyyun free democrats da the greens sun yi kakkausan suka a game da wannan hadin guiwa. Sassan biyu sun cimma daidaituwa ta yin karba-karba ne tsakanin ‚yan takarar da suka tsayar, inda bayan shekaru biyu da rabi wani daga rukunin ‚yan mazan-jiya zai maye gurbin Josep Borrell dan socialist, inda ake kyatata zaton cewar Hans-Gert Pöttering dan jam’iyyar Christian Democrats daga nan Jamus, shi ne za a nada bayan shekaru biyu da rabi masu zuwa. A karon farko wakilan sabbin kasashen da aka karbesu a Kungiyar tarayyar Turai a farkon watan mayun da ya wuce sun halarci zaman taron majalisar ta Turai tare da cikakken ikon kada kuri’a. Wani abin lura kuwa shi ne karuwar da aka samu a game da yawan wakilan jam‘iyyu masu dari-dari ko kyamar manufofin hadin kan Turai a majalisar ta Strassburg. Sai dai kuma a sakamakon rarrabuwar hankula ba a samu hadin kai tsakanin wadannan jam’iyyu ba ballantana su yi wani tasiri na a zo a gani a majalisar. Har yau ‚yan mazan-jiya ne ke da angizo tare da wakilai 268 sai kuma ‚yan socialist dake da wakilai 200, sannan ‚yan liberals tare da wakilai 88 da the greens dake da wakilai 42. A jawabinsa na mubaya’a Josep Borrell yayi alkawarin kamanta adalci a tsakanin dukkan jam’iyyun dake da wakilci a majalisar, kuma muhimmin abin da zai sa gaba shi ne ganin an amince da daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin illahirin kasashen KTT. Ya ce zai yi bakin kokarinsa domin ganin cewar majalisar Turai ta bi diddigin dukkan matakan da za a dauka na amincewa da daftarin tsarin mulkin hatta a kasashen da za a kada kuri’ar raba gardama akansa. A karkashin shugabancinsa majalisar ta Turai zata yi bakin kokarinta wajen cimma daidaituwa akan tsarin albashi da alawos-alawos din wakilanta. A jibi alhamis idan Allah Ya kaimu wakilan majalisar Turan su 732 daga kasashe 25 zasu kada kuri’a domin nada shugaban hukumar zartaswa ta KTT, wanda shi ne mukami mafi tasiri a kungiyar. Dan takara daya kwal da za a kada kuri’a kansa shi ne Jose Manuel Durao tsofon P/M kasar Portugal dake da ra’ayin mazan jiya. A nan ma akwai jita-jitar cewa an cimma daidaituwa ne tsakanin ‚yan mazan-jiya da ‚yan socialist domin nadinsa akan wannan mukami.