1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Turai na binciken CIA.

January 23, 2006

Tun da labarain kafa sansanonin kungiyar leken asirin Amirka, wato CIA a nahiyar Turai ya fito fili ne, kafofin hukumomi da dama na kasashen nahiyar suka fara gudanad da bincike a kan batun. A halin yanzu dai, babban sakataren majalisar mashawarta ta tarayyar Turai, ya ce shi ma ya fara hudanmad da nasa binciken.

https://p.dw.com/p/Bu2D
Majalisar mashawarta ta nahiyar Turai, a birnin Starßburg.
Majalisar mashawarta ta nahiyar Turai, a birnin Starßburg.

Terry Davis, babban sakataren Majalisar Mashawarta ta kungiyar Hadin Kan Turai, ya aike da wata takardar tambayoyi ga shugabannin kasashen 46, mambobin majalisar, inda ya bukace su, su ba shi amsar tambayoyinsa kafin ran 21 ga watan Fabrairu mai zuwa. Gundarin abin da babban sakataren ke son ya sani shi ne, wai shin, duk kasashen za su iya tabbatar masa cewa tun shekara ta 2002, ba a taba samun wasu fursunonin da aka tsare a kurkuku a cikin harabobinsu ba tare da izinin kotu ba, ko ma aka yi ta nuna musu azaba iri-iri? Kuma, kasashen sun tabbatar cewa, kungiyar leken asirin Amirka ba su yi amfani da kasashensu wajen jigilar fursunoni zuwa wasu kasashen ketare inda suke ta nuna musu azaba ba ?

A ganin Terry Davis dai, idan aka gano cewa wasu gwamnatocin kasashen da ke da wakilci a majalisar, sun tallafa wa kungiyar leken asirin Amirka, wato CIA, a ko wace hanya, wajen gallaza wa fursunonin da suke tsare da su, to za a iya zarginsu da take kudurorin kare hakkin dan Adam da duk kasashe mambobin majalisar mashawartan suka amince da su. Game da wannan binciken da yake gudanarwa dai, babban sakataren ya bayyana cewa:-

„Ina da cikakken ikon gudanad da bincike, don tabbatad da cewa kasashe mambobin kungiyar EUn sun kiyaye ka’idojin da aka yarje a kansu ko kuma a’a. Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka taba yin amfani da wannan ikon ba. A cikin shekaru 50 da suka wuce, an gudanad da bincike kusan 80.“

Sai dai, Terry Davis ya kara da cewa, dalilan da suka janyo gudanad da binciken a da, ba su kai na yanzu tsamari ba. Sabili da haka ne kuwa, majalisar mashawartan ta fi dacewa wajen gudanad da wannan aikin. Saboda angizonta ya yadu ne zuwa duk kasashen Turai ban da kasar Bellaruss, amma har da kasashen Romaniya da Macedoniya, inda ake zaton kungiyar ta CIAn na da sansanoninta.

Idan dai binciken Terry Davis ya tabbatad da zaton da ake yi, na cewa wasu kasashen Turai sun mara wa kungiyar ta CIA baya, wajen gudanad da wannan danyen aikin na gallaza wa fursunoni, to wajibi ne bisa ka’ida, ministocin harkokin wajen kasashen da ke cikin majalisar mashawartan, su yi tofin Allah tsine ga wadannan kasashen, su kuma sanya musu takunkumi. Bugu da kari kuma, inji Babban sakataren, mai yiwuwa a daukaka karar kasashen da aka same su da laifin, gaban babban kotun kare hakkin dan Adam na tarayyar Turai, da ke birnin Straßburg.

Terry Davis dai na hasashen cewa, kungiyar NATO ma na da hannu a cikin danyen aikin da CIA din ta aikata. Saboda bisa cewarsa, rundunar dakarun kare zaman lafiya ta KFOR a lardin Kosovo, wadda ke karkashin laimar kungiyar ta NATO, tana da wasu sansanoni, inda take tsare fursunoni, amma wadanda aka hana wa jami’an majalisar mashawartan damar shiga ciki don su gudanad da bincike. Duk da cewa, kwamitin sa ido don hana azabtad da fursunoni na majalisar na da ikon binciken ko wane sansani da ke kan harabar Turai. Tun shekara daya da rabi da suka wuce ne dai, babban sakataren, na majalisar mashawarta ya yi ta kokarin samun bayanai daga kungiyar ta NATO, amma ba tare da samun wata nasara ba. Kamar yadda ya bayyanar:-

„Babu dai wata hanyar matsa musu lamba. Amma tun watanni 18 da suke wuce ne muke ta kokarin samun izinin shiga cikin sansanonin da ke hannun rundunar KFOR a lardin Kosovo. Tun ma kafin wannan batun CIAn ya fito fili. Ina dai zaton cewa a can ma, akwai gidajen yarin CIA din, sai dai ba ni da cikakken bayani ne a kansu.“

Ita Amirka ma na tura wakilanta zuwa tarukan majalisar mashawartan ta nahiyar Turai, a matsayin `yan kallo. Amma Terry Davis ya ce, ba shi da ikon yi wa gwamnatin Amirkan tambaya . Yana da angizo ne kawai a kan cikakkun mabobi, amma ba `yan kallo ba. Sabili da haka, da wuya ya sami wani hadin kai daga birnin Washington, don gudanad da bincikensa.