Majalisar Turai na binciken CIA - 2. | Siyasa | DW | 24.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Majalisar Turai na binciken CIA - 2.

Jami'in da majalisar mashawarta ta taryyar Turai ta nada don ya gudanad da bincike kan jigilar fursunoni da kuma azabta musu da ake zargin kungiyar leken Asirin Amirka, wato CIA da yi, Dirk Marty, ya gabtad da rahotonsa na biyu a kan sakamakon da ya samu har ya zuwa yanzu.

Dick Marty, a lokacin da yake gabatad da rahotonsa ga majalisar.

Dick Marty, a lokacin da yake gabatad da rahotonsa ga majalisar.

Bisa ka’idojin shari’a dai, ba a sami wasu karfafan hujjoji da za a iya zargin kungiyar leken asirin Amirka da aikata laifuffukan azabtad da fursunoni ba, ko ma kafa wasu sansanonin sirri a nahiyar Turai, inda ake zaton suke aikata wadannan munanan aikin. Haka ne dai tsohon babban lauyan gwamnatin kasar Switzerland, Dick Marty, ya bayyana sakamamon binciken da ya gudanar har zuwa yanzu, a kan tuhumar da ake yi wa kungiyae leken asirin ta Amirka. Amma ya kara da cewa, ya samo alamu da karin bayanai, wadanda ke karkata zuwa tabbatad da wannan zargin. A ganinsa dai, babu shakka, jami’an kungiyar ta CIA, da mukarrabansu, sun sace mutane kuma sun yi jigilar fursunonin da suke tuhumarsu da gudanad da ayyukan ta’addanci, a nan Turai duk ba bisa ka’ida ba. Bugu da kari kuma, ya ce akwai sansanonin da suke yi wa wadannan fursunonin tambayoyi, tar da gallaza musu. Dick Marty ya ci gaba da bayyana cewa:-

„Akwai majiyoyi da dama da suka tabbatar mana da wanzuwar wadannan sansanonin nan sirri. Kuma labarai ne ingantattu wadanda za a iya dogara a kansu. Ina tabbatar muku cewa, wadannan majiyoyin masu tushe ne kuma labaransu na kwarai ne. Sai dai, ba zan iya bayyana muku sunansu ba a nan.“

A ganin Marty dai, ba zai taßa yiwuwa a ce mahukuntan kasashen da aka gudanar wadannan mummunan aikin ba su san da kasancewar kungiyar CIA din a harabobinsu ba. Jami’in dai ya ambaci lardin Kosovo ne, inda rundukar kare zaman lafiyar nan ta KFOR ta girke dakarunta. A nan dai, inji Marty, akwai sansanonin kungiyar NATO, wadanda aka hana masu bincike daga majalisar mashawarta ta tarayyar shiga cikinsu. Wadannan ayyukan dai, ba za a iya takaita su kawai a kasashen Romeniya da Poland ba:

„Kuskure ne a takaita kasancewar sansanonin a kasashen Poland da Romeniya kawai. Ba kuma daidai ba ne a yi ta sukar wadannan kasashen kawai. Wannan taßargazar dai ta shafi duk Turai ne gaba daya.“

A halin yanzu dai, ana zaton cewa, a nan Jamus ne kungiyar leken asirin Amirkan ta fi yin amfani da filayen jiragen saman soji, wajen jigilar fursunonin. Poland da Romeniya kuma, sun sha yin watsi da zargin da ake yi musu na cewa, akwai sansanonin CIA din a kasashensu.

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleeza Rice, a wata ziyarar da ta kai a hedkwatar kungiyar NATO a cikin watan Disamban bara, ta tabbatar cewa, tun `yan shekarun da suka wuce ne dai, Amirkan ke ta jigilar fursunoni a nahiyar Turai. Amma ta ce manufar kasarta ce hana kai fursunoni a kasashen da ta san za a azabtad da su. Wato jigilar fursunonin kawai, a ganin Amirka, bai take wata doka ba.

Amma shi Dick Marty, yana watsi da wannan ra’ayin. Sai dai, ya kuma zargi kasashen nahiyar da dama da rashin ba da hadin kai, wajen kokarin da ake yi na haskaka wannan lamarin.

A halin yanzu dai, Majalisar mashawartar tarayyar Turai, ta bai kasahe mambobinta ne har zuwa ran 21 ga watan Fabrairu mai zuwa, don su amsa tambayoyin da babban sakataren majalisar ya aike musu da su a rubuce, game da hada-hadar da kungiyar CIA din ta yi ta yi a kasashensu. Sai dai bayan an sami amsoshin wadannan tambayoyin ne Dick Marty zai iya ba da cikakken rahotonsa a kan wannan batun.