1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Nijar ta yi zama na musamman

Abdoulaye Mamane AmadouMarch 1, 2016

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta yi zama na musamman a matsayin zaman karshe da majalisar za ta yi kafin sababbin zababbun 'yan majalisa.

https://p.dw.com/p/1I4u7
Niger Kongresszentrum in Niamey
Hoto: DW/M. Kanta

Zaman taron na majalisar dokokin na a matsayin na karshe da majalisar za ta yi bisa la'akari da wa'adin majalisar da ke shirin karewa a 'yan kwanaki masu zuwa inda tsoffin 'yan majalisar za su tattara domin bai wa wasu sababbin fage domin ci gaba da aikin majalisar har na tsawon wasu shekaru biyar masu zuwa.


'Yan majalisar za su dukufa ne a kan wasu mahimman dokokin da suka shafi kudi da tallafin da gwamnatin kasar ke fatar ganin sun shigo a aljihunta, tun daga farko-farkon wannan shekarar hukumomin kolin na bangaren zartarwa suka rattaba hannu kana kuma suke jiran isowar majalisar ta dokoki don amincewa da su.

Niger Wahl Wähler in Niamey
Hoto: DW/A. Amadou

Zakari Oumarou shugaban rukunin yan majalisar dokokin jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki kuma ya nuna muhimmancin matkin da suka dauka.

Tun kafin wannan lokacin dai wata takaddama ta barke a tsakanin 'yan majalisa kan batun soma zaman na majalisar inda aka samu rarrabuwar kawuna kan wa'adi da ma tasirin da zaman majalisar zai yi bisa la'akari da karatowar yakin neman zabe, abubuwan da suka kai ga shugaban majalisar tuntubar kotun tsarin mulki wanda daga bisani kotun ta halattar da zaman na majalisar duk da karshen wa'adin da 'yan majalisar suke da shi. To amma sai dai zaman ba zai taba wani tasiri ba inji Salah Amadou Hassan dan majalisar dokokin jam'iyyar Moden Lumana Afrika mai adawa.

Niger Konferenz- und Kongresszentrum "Palais des Congres" in Niamey
Hoto: DW/D. Köpp


Sai dai tuni wasu masu sharhi a fagen siyasar kasar suka fara rade-radin yiwuwar shigar da bukatar tsige gwamnati a zaman na majalisa da ma kaurace wasu dokokin da ake ganin za su iya taimakon gwamnatin daga bangaren 'yan majalisa na bangaren adawa. Sai dai a cewar dan majalisar dokokin jam'iyyar MNSD Nasara Lamidou Moumouni wannan ba abin da ke damun 'yan adawa ba ne a yanzu.


A tsawon wa'adin shekarunta biyar da ke shirin karewa a ranar 14 ga wannan watan majalisar ta dokoki ta rattaba hannu da jefa kuri'a a kan wasu dokoki 318 da ajiye bukatar tsige shugaban gwamnati har sau biyu da gayyatar ministoci domin bayar da bahasi har sau 16 da karkafa wasu tarin kwamitoci domin binciken wasu matsaloli da suka addabi al'ummar kasar.