Majalisar ministocin Lebanon ta amince da kafa kotu ta binciken mutuwar Rafik al-Hariri | Labarai | DW | 25.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar ministocin Lebanon ta amince da kafa kotu ta binciken mutuwar Rafik al-Hariri

Majalisar zartaswa ta Lebanon ta amince a taronta na gaggawa data kira yau kan kotun da MDD zata kafa game da kisan Hariri,duk kuwa da adawa da membobin majalisar dake goyon bayan Syria sukayi.

Tun farko dai firaminista Siniora ya yi kira ga ministoci 6 masu goyon bayan Syria wadanda suka fice daga majalisar makonni 2 da suka shige da su koma cikin majalisar don amincewa da tabbatar da kafuwar wannan kotu.

Amma ministocin sunyi biris da shi bayan da manyan bagrorin adawa 2 sun baiyana a fili cewa zasu koma majalisar,idan firaminisatn ya mutunta yarjejeniyar kasar wadda ta baiwa dukkanin addinai da kabilu na kasar samun wakilci a gwamnati.