Majalisar ministocin Jamus ta amince da tura dakarunta zuwa Kongo | Labarai | DW | 17.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar ministocin Jamus ta amince da tura dakarunta zuwa Kongo

Majalisar ministocin tarayyar Jamus ta amince da girke dakaru kimanin 800 na rundunar sojin kasar wato Bundeswehr a JDK a karkashin inuwar KTT. Dakarun Jamus din sun hada da sojoji 500 da likitocin soji 280,wadanda za su yi aiki karkashin rundunar kiyaye zaman lafiya na kungiyar EU. EU dai zata girke sojoji dubu 1 da 500 don tabbatar da tsaro a lokacin zabukan da zai gudana a Kongo a ranar 30 ga watan yuli. Yanzu haka dai ya rage majalisar dokoki ta Bundestag ta albarkaci wannan matakin. Tuni dai wasu ´yan jam´iyun adawa a majalisar suka fara sukar shirin da kakkausar harshe. Daya daga cikinsu kuwa shi ne Wolfgang Gerhardt tsohon shugaban jam´iyar FDP wanda ya bayyana rashin amincewar sa yana mai cewa:

„A namu ganin dai, wannan shiri ne da ba a tsara shi sosai kamar yadda ya kamata ba. Kuma a huskar siyasa, bamu taɓa shiga cikin irin hali kamar wannan ba. Da farko, tun ba a san ma inda za a mai da alƙibla ba, shugaban gwamnatin tarayya ta tabbatar wa shugaban Faransa cewa a shirye muke mu tura dakarun. A lokacin, ba mu da wata masaniya kan yadda ɗaukin zai kasance. An ce a birnin Kinshasa kawai za a girke dakarun. To amma idan aka yi la’akari da girman Kwangon, da halin da take ciki a yanzu, da kuma yawan ’yan takara a zaɓen, zai yi wuya a yi hasashen inda rikici zai ɓarke, da kuma ɗan takaran da zai fi bukatar kare lafiyarsa.“

Ana sa rai a ranar juma´a mai zuwa majalisar zata yi wani zama na musamman don yin muhawwara akan wannan batun kafin ta yanke ta ta shawarar.