Majalisar ministocin Jamus ta amince da tsawaita aikin sojojin ƙasar a Afghanistan | Labarai | DW | 19.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar ministocin Jamus ta amince da tsawaita aikin sojojin ƙasar a Afghanistan

Gwamnatin tarayyar Jamus ta amince ta kara wa´adin aikin da sojojin ta ke yi a Afghanistan. A yau a birnin Berlin majalisar ministocin shugabar gwamnati Angela Merkel ta kada kuri´ar tsawaita aikin sojojin na rundunar Bundeswehr da shekara daya a karkashin inuwar rundunar kasa da kasa a Afghanistan wato ISAF. Bugu da kari majalisar ministocin ta kuma amince da tura jiragen saman bincike a Afghanistan. Yanzu haka dai Jamus na da sojoji dubu 3 wadanda ke aikin sake gina Afghanistan. A gobe alhamis majalisar dokoki zata fara muhawwara akan wannan mataki sannan ta kada kuri´a kai a ranar 12 ga watan oktoba.