Majalisar Kasashen Turai, ta kudurci buda bincike a kan batun Pirsinonin CIA | Labarai | DW | 23.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Kasashen Turai, ta kudurci buda bincike a kan batun Pirsinonin CIA

Majalisar hukumar turai, ta kudurci gudanar da bincike, a game da jita jitan nan, mai bayyana cewa, hukumar leken assiri ta Amurika wato CIA, ta yi jiggilar wasu Pirsinoni, da ta zarga da aikata ta´adanci, a wasu kasashen turai, da su ka hada da Spain, Portugal, Suedeen da Finlande.

Sakataran gudanarwa na hukumar ya gayyaci kasashe 45 da abin ya shafa, da su bada hadin kai domin gano hakikkanin gaskiyar al´amarin.

Nahiyar turai ba ta laminta ba ayi anfani da daya daga kasashen ta, domin tozarta jama´a inji sakataran gudanarwa na Majalisar hukumar turai Terry David.

Kamin buda wannan bincike kasashen da a ka zarga da Amurika, ta yi anfani da tashoshin jiragen su, na sama, sun karyata batun.