1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Jihar Bayelsa a Nigeria ta dauki mataki...............

Majalisar dokokin jihar Bayelsa ,dake kudancin Nigeria ta amince da gagarumin rinjaye na nada mataimakin gwamnan jihar, wato Dr Goodluck Jonathan a matsayin mai rikon mukamin gwamnan jihar.

Daukar wannan mataki dai daga bangaren yan majalisun dokokin ya biyo bayan ci gaba da tsare gwamnan jihar ne da jamian yan sandan Biritaniya keyi, bisa zargin shiga kasar da kudade da suka wuce ka´ida.

A cewar kakakin gwamnatin kasar,wato Solomon Banigo,daukar wannan mataki da majalisar dokokin tayi zai cike gibin gudanar da mulki a jihar ta Bayelsa.

Idan dai za a iya tunawa, jamian yan sandan na Biritaniya sun cafke gwamna DSPA ne a ranar 15 ga watan satumba na wannan shekara a filin jirgin saman hizru dake birnin London, bisa zargin shigowa kasar da kudade da suke wuce ka´ida