Majalisar Iraƙi ta amince da maido da yan jam′iyar Baath aikin gwamnati | Labarai | DW | 12.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Iraƙi ta amince da maido da yan jam'iyar Baath aikin gwamnati

Majalisar dokokin Iraƙi ta amince da wani ƙudurin doka dake neman maido da tsoffin magoya bayan jam’iyar Baath kan aiyukansu na gwamnati. Wannan muhimmin mataki dai zai kai ga sasanta tsakanin jama’ar ƙasar. Dokar ta nemi a sassauta ka’idojin da aka shimfiɗa kan tsoffin magoya bayan jam’iyar marigayi Saddam Hussein don cike giɓin gurabun aiki na gwamnati.