MAJALISAR DUNKIN DUNIYA DA ZABEN IRAKI. | Siyasa | DW | 16.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MAJALISAR DUNKIN DUNIYA DA ZABEN IRAKI.

Majalisar dunkin duniya na shirin fadada ayyukanta a kasar Iraki dake cigaba da kasancewa cikin rikici,gabannin zaben kasa baki daya da ake saran zai gudana a watan gobe.

Sakataren majalisar Dunkin Duniya Kofi Annan.

Sakataren majalisar Dunkin Duniya Kofi Annan.

Bayan dakatar da ayyukanta sakamakon rikice rikice dayaki ci yaki cinyewa a kasar Iraki,inda ake cigaba da zubar da jinin jamaa,MDD ta sanar da manufarta na sake fadada ayyukan ta wannan kasa dake shinrin gudanar da zabe a jarshen watan gobe.

Kakakin Majalisar Fred Eckhard ya fadawa taron manema labaru cewa zaa fadada yawan manyan jamian daga 59 dasuke a yanzu,sai dai bai ambaci adadin wanda zaa kara ba.Hukumar lura da harkokin tsaro na Mdd ta kayyade wannan adadin ,sakamakon halin dardar da wannan kasa ke ciki,inda daga watan maris zuwa yanzu dakarun mamaye a karkashin jagorancin Amurka sama da 1,200 suka sheka lahira,banda dubban fararen hula.

A wata wasikar hadin gwiwa da kungiyar tare da wata kungiyar maaikata dake aiki a karkashin majalisar suka rubutawa sakatare General Kofi Annan a watan daya gabata,sunyi kira da dakatar da tura maaikata zuwa Irakin,kana a janye wadanda kecigaba da kasancewa a kasar.Kungiyoyin biyu dai sun nuna bukatarsu na taimakawa Iraki dake neman agaji ta kowane bangare,sai dai kuma bazasu iya cigaba da salwantar da rayukan jamiansu ba saboda rashin tsaro dake barazana a wannan kasa dama dukkan wadanda ke ciki.Kungiyoyin biyu dai na wakiltan maaikata sama da dubu 60,dake karkashin MDD a sassa daban daban na duniya.

Yanzu haka dai majalisar nada jamianta na ketare kimanin 210 a Iraki,wadanda suka hadar da jamian kariya 150,da kwararru ta fannin zabe 60.A karkashin wannan sabon shirin dai,ana kyautata zaton cewa majalisar zata kara yawan kwararru ta fannin zaben da wasu maaikata da wajen kashi 30.

Kakakin majalisar yace Mr Kofi Annan zai fadada ayyukan tallafi na majalisar ,domin tallafawa Irakin gudanar da zabe ba tare da wata matsala ba,musamman ayankunan Basra da Erbil dake fama da rikici.Mr Annan a halin yanzu na shirin tura jamian sharan fage zuwa wadannan yankunan domin ganewa idanunsu halin da ake ciki,da samarda matsuguni wa jamian da zaa tura gabannin wannan zaben.Kakakin yace bawai zasu lura da yadda zaben zai kasance bane,sai dai zasu bada tallafi na kayan aiki.

A baya dai sakataren MDD yaki amincewa da tura jamiansa zuwa Irakin,inda ya zuwa yanzu yake cigaba da fuskantar matsin lamba daga Amurka da ita kanta Irakin.

MDD ta janye maaikatanta 650 daga Iraki ,bayan harin kunar bakin wake da aka afkawa gininta a Bagadaza a watan Augustan shekara ta 2003.Harin daya kashe mutane 22 harda babban jakada Sergio Vieira de Mello.

A yanzu dai manazarta na ganin cewa babu wani abu da Mdd zata tabuka yanzu daya rage makonni 6 kachal a gudanar da zaben Irakin.

Zainab A Mohammed.