Majalisar dokokin Venezuela ta amince da yiwa tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima
November 3, 2007Talla
Majalisar dokokin kasar Venezuela ta ba da amincewarta ta karshe kan jerin canje canje da za´a yiwa kundin tsarin mulkin kasar wanda zai karfafa ikon shugaba Hugo Chavez. Hakan kuwa ya hada da dage wa´adin mulki sau biyu ga shugabanni sai kara yawan shekarun wa´adin daga 6 zuwa 7. Wakilai 160 daga cikin 167 daukacin su magoya baya shugaba Chavez suka amince da canje canjen, wadanda ´yan kasar zasu kada kuri´ar raba gardama a kai a farkon watan desamba. Bugu da kari za´a bawa jami´an tsaro ikon tsare ´yan kasar ba tare da wata tuhuma ba sannan za´a tace labarai a lokacin aukuwar wani bala´i ko kafa wasu dokoki na tabaci.