1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Nijeriya ta amince da naɗin mataimakin shugaban ƙasar.

May 18, 2010

Majalisar dokokin Nijeriya ta yarda da naɗin Namadi Sambo a matsayin mataimakin shugaban ƙasar

https://p.dw.com/p/NR8Q
Hoto: DW

Ɗazunnan ne majalisar dokokin tarayyar Nijeriya ta amince da naɗin gwamnan jihar Kaduna Namadi Sambo a matsayin mataimakin shugaban ƙasar. Dukkan majalisun biyu, wato ta dattijai da kuma ta wakilai ne suka yi na'am da sunan mutumin da shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Jonathan ya aike musu domin ɗarewa kan muƙamin mataimakin shugaban ƙasar. Gwamna Namadi Sambo, wanda a yanzu kuma za'a rantsar a matsayin mataimakin shugaban Nijeriya, an haifeshi ne a ranar biyu ga watan Agustan shekara ta 1952 a birnin Zazzau dake jihar Kaduna a yankin arewacin Nijeriya, inda kuma ya yi karatu a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya kuma riƙe muƙamin kwamishina a jihar Kaduna - a ma'aikatun da suka haɗa dana harkokin Noma, dana ayyuka da guidaje, da kuma na harkokin sufuri. Yana da aure da 'ya'ya shidda.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umar Aliyu