Majalisar dokokin kasar kanada ta kada kuriár rashin amanna da gwamnatin P/M Paul Martins. | Labarai | DW | 29.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dokokin kasar kanada ta kada kuriár rashin amanna da gwamnatin P/M Paul Martins.

Gwamnatin kasar Kanada karkashin jagorancin P/M Paul Martins ta sha kaye a kuriár rashin amanna da yan majalisun dokokin kasar suka kada. Gwamnatin dai ta fada cikin dambarwa ta tabargazar cin hanci da rashawa. A halin da ake ciki P/M zai bukaci rushe majalisar dokokin da kuma sanya ranar gudanar da sabon zabe. Kuriár jin raáyin jamaá na nuni da cewa Jamíyar Liberal ta P/M ka iya samun kuriú masu yawa to amma da kyar ne idan zata sami gagarumin rinjayen da ake bukata. Gwamnatin wadda ta sami watanni goma sha bakwai kacal akan karagar mulki ta gaza shawo kann tabargazar cin hancin wanda ya samo tushe daga tsohuwar gwamnatin ta Liberal.