Majalisar dokokin Jamus ta fara muhawwara game da girke dakarun kasar a Kongo
May 19, 2006Gwamantin tarayyar Jamus ta kare shirin ta na girke dakarun kasar a JDK, shirin da ke shan kakkausar suka daga jam´iyun adawa. A wani jawabi da yayiwa majalisar dokoki ta Bundestag ministan harkokin waje Frank-Walter Steinmeier ya ce Jamus na da kwakkwarar hujjar girke dakarun ta a Kongo. Kasar dai na shirin ba da gudammawar sojoji 780 a karkashin rundunar da kungiyar EU zata tura Kongo don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a lokacin zaben da zai gudana a Kongon a ranar 30 ga watan yuli. Za´a girke wasu daga cikin sojojin ne a yankunan dake kusa da babban birnin kasar wato Kinshasa. A muhawwarar da majalisar dokoki ta fara yau dangane da batun tura sojojin an Bundeswehr a Kongo, ministan harkokin wajen yayi kira ga ´ya´yan majalisar da suka kada kuri´ar amincewa da wannan shiri.
“Idan aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kongo, to ko shakka babu yankin gabashin nahiyar Afirka gaba daya zai fita daga wani yanayi na yaki da rikice rikice da kuma wahalhalu iri dabam-dabam da suka addabi al´umar wannan yanki. Saboda haka ya zama wajibi a gare mu, mu amsa kiran Majalisar Dinkin Duniya don tabbatar da tsaro a lokacin gudanar da zaben a ranar 30 ga watan yuli.”
A ranar daya ga watan yuni majalisar dokokin ta Jamus zata kada kuri´a akan wannan batu.