1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta fara zaman ta

October 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvOs

A yau wata guda daidai bayan kada kuri´a, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta yi zamanta na farko don fasalta kanta. Tare da gagarumin rinjaye na wakilai 614 an zabi dan jam´iyar CDU Norbert Lammert a matsayin sabon shugaban majalisar. Yanzu haka dai dan jam´iyar ta CDU ya maye gurbin dan SPD Wolfgang Thierse. Zaman majalisar a yau ya kawo karshen wa´adin gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens, karkashin shugaban gwamnati mai barin gado Gerhard Schröder wanda ya sha kaye a zaben ´yan majalisar dokoki da ya gudana a ranar 18 ga watan satumba. A yau talata ce kuma shugaban tarayyar Jamus Hosrt Köhler zai ba wakilan tsohuwar majalisar zartaswa shahadar kammala aiki. To sai dai har yanzu gwamnatin Schröder ce zata ci-gaba da jan ragamar mulki a Berlin har zuwa lokacin da za´a nada sabuwar shugabar gwamnati, wato Angela Merkel ´yar jam´iyar CDU.