majalisar dokokin Faransa ta amince da sabuwar dokar zaman baki
July 1, 2006Talla
Bayan taron kasa yanzu haka dai majalisar dokokin Faransa ta albarkaci sabuwar dokar zaman baki a cikin kasar wadda ake takaddama akai bayan kungiyoyin kwautata zaman baki sun shafe makonni suna zanga-zangar nuna adawa da dokar. Sabuwar dokar wadda ministan cikin gida mai ra´ayin rikau Nicolas Sarkozy ya gabatar, zata tsaurara shigar baki wadanda ba su da kwarewa cikin kasar yayin da kwararru kuma zasu samu takardun izinin zama a kasar na tsawon shekaru 3 da farko. Ga mai sha´awar samun izinin zama na dindindin a kasar kuwa dole ne ya koyi harshen faransanci. Ministan cikin gida wato Sarkozy ya ce tarzomar matasa da aka fuskanta a cikin watan nuwamban bara ta nunar a fili bukatar da ke akwai wajen tsaurara dokokin zaman baki a Faransa.