Denmak ta haramta saka burqa
May 31, 2018Talla
Dokar wacce 'yan majalisun dokokin 75 suka amince da ita yayin guda 30 suka hau kujerar naki,ta tanadi yin hukuncin na cin tara ta kudade kusan Euro 150 ga wada aka samu da laifin sanya burqa. Nan gaba a ranar daya ga watan Augusta dokar za ta fara aiki, bayan da kasashen Faransa da Beljiyam da Austriya suma suka amince a rin wannan doka.