1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MAJALISAR DOKOKI TA BUNDESTAG TA YI MUHAWARA KAN DAGE TAKUNKUMIN SAYAD DA MAKAMAI DA AKA SANYA WA KASAR SIN.

Bisa bukatar da jam'iyyun adawa a majlisar dokoki ta Bundestag suka yi ne, aka bude wata muhawara mai tsanani a zauren taron majalisar da ke birnin Berlin. Shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder ya kare matsayinsa na neman a dage takunkumin. Su ko `yan adawa sun ce ko wane mataki za a dauka ma, dole ne sai an tuntubi Amirka.

Shugaba Schröder a lokacin da yake jawabi a majalisar.

Shugaba Schröder a lokacin da yake jawabi a majalisar.

Shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder ya dage kan matsayinsa na neman Kungiyar Hadin Kan Turai ta soke takunkumin sayad da makaman nan da ta sanya wa kasar Sin tun shekaru 15 da suka wuce. Da yake nasa jawabin a muhawarar da jam’iyyun adawa na majalisar dokoki ta Bundestag suka nemi a yi a kan wannan batun, shugaba Schröder ya bayyana cewa, takunkumin ba shi da wani amfani kuma a halin da muke ciki yanzu. Amma a wannan karon dai, ba shi da goyon baya. Jam’iyyar kawance ta Greens, wadda ke cikin gwamnatin hadin gwiwar da shugaba Schröedrn ke yi wa jagoranci, ta juya masa baya. Kai har wasu `yan jam’iyyarsa ta SPD din ma sun ce ba sa goyon bayan wannan matakin.

A ganin shugaba Schrödern dai, dage takunkumin ba zai sa a habaka yawan cinikin sayad da makamai ga kasar Sin ba. Babu shakka, inji shugaban, a cikin `yan shekarun bayan da suka wuce, an sami kyakyawan sauyi a kasar ta Sin. Bugu da kari kuma, kasar na da muhimmanci kwarai ga Jamus, a huskar kasuwanci. Sabili da haka ne dai yake ganin kamata ya yi Jamus da inganta huldodinta da Sin. To ba za a sami sassaucin tsamari ba kuwa idan aka ci gaba da shimfida mata shinge da ke hana ruwa gudu a dangantakar da ke tsakaninsu.

Duk da adawar da suke nunawa ga matsayin Gerhard Schröder dai, jam’iyyun adawan ma sun amince da muhimmancin da Sin ke da shi ga huldodin cinikayya da Jamus. Sai dai suna dari-dari da matakin radin kan da Jamus za ta iya dauka ita kadai na soke takunkumin. Mataimakin shugaban jam’iyyar adawa ta CDU a majlisar dokoki ta Bundestag, Wolfgang Schäuble, ya bayyana cewa ko da kungiyar EU ce ma za ta amince da dage takunkumin, bai kamata ta yi haka ita kadai ba. Wajibi ne ta tuntubi Amirka tukuna. Amma a nasa ganin ma, yanzu ba lokaci ba ne na dage takunkumin. Har ila yau dai, inji shi, ana take hakkin dan Adam a kasar ta Sin, duk da kambama kanta da kasar ke yi na cewa an sami gagarumin ci gaba, a wannan huskar.

Shi dai shugaba Schröder, bai bata lokaci wajen yin doguwar muhawara kan wannan batun ba. Sabili da haka ne kuwa, duk aka yi ta jiran jawabin da ministan harkokin waje Joschka Fischer zai yi. Amma shi ma da ya sami damar magana, bai tabo wannan batun kamar yadda ake yi masa kallo a nan Jamus ba. Ya yi kira ne ga Sin da ta dau matakan gaggawa wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar nan ta amincewa da kudurorin kare hakkin dan Adam a kasarta.

Hakan dai ya fusatad da shugaban jam’iyyar adawar Angela Merkel, wadda ta yi masa suka da rashin bajinta, da kuma rashin sanin irin kamun ludayin da zai yi a kan wannan batun.

Daga `yan jam’iyarsa ta SPD ma, shugaba Schröder bai sami cikakken goyon baya ba. Sai ministan tattalin arziki Wolfgang Clement da ministan tsaro Peter Struck ne suka fito fili suka ce sun yi amanna da matsayin da shugaban gwamnatin ya dauka.

 • Kwanan wata 14.04.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvcR
 • Kwanan wata 14.04.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvcR