Majalisar Dinkin Duniya zata rage yawan taimakon abinci a Sudan | Labarai | DW | 29.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya zata rage yawan taimakon abinci a Sudan

Karancin kudaden taimako daga kasashe masu ba da agaji, ya sa a dole MDD ta rage yawan taimakon kayan abinci da take bawa al´umar kasar Sudan dake cikin halin ni ´ya su. Wata mai magana da kungiyar samar da abinci ta MDD ta ce daga mako mai zuwa za´a rage kashi 50 cikin 100 na yawan abincin da ake ba mutane kimanin miliyan 6.1 a kowace rana. Jami´ar ta ce daukar wannan matakin ya zama dole don ba su da wani zabi. Daga cikin wadanda wannan matakin ya shafa akwai mutane miliyan 3 na lardin Darfur dake yammacin Sudan.