Majalisar Dinkin Duniya zata janye daruruwan ma´aikatanta daga Kodivuwa | Labarai | DW | 27.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya zata janye daruruwan ma´aikatanta daga Kodivuwa

Saboda fargabar sake aukuwar tashe tashen hankula Majalisar Dinkin Duniya zata janye ma´aikatan ta kimamnin 400 daga Ivory Coast wato Kodivuwa. To amma kafin a dauki wannan matakin sai shugaban tawagar MDD a Ivory Coast yayiwa kwamitin sulhu bayani dalla-dalla irin halin da ake ciki a kasar dake yankin yammacin Afirka. A makon da ya gabata MDD ta yi barazanar kakabawa Ivory Coast din takunkumi, bayan wani bore da magoya bayan shugaba Laurent Gabgbo suka tayar akan sojojin MDD dake birnin Abidjan. Duk da yarjejeniyar samar da zaman lafiya da aka kulla, har yanzu kasar ta rabu gida biyu inda dakarun gwamnati ke iko da kudu yayin na ´yan tawaye ke rike da aewacin kasar.