1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dinkin duniya tayi kira da gagauta tsagaita wuta a Somalia

March 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuP6

Majalisar dinkin duniya tayi kira da dakatar da tarzoma a Mogadishu ba tare da bata lokaci ba,inda fada ya barke tsaknin sojin sa kai da dakarun kasar dana Habasha.

Akalla mutane 24 suka rasa rayukansu daruruwa kuma suka samu raunuka yayinda wasu dubbai kuamsuka tsere daga birnin na Moagdishu.

Rahotanni sunce tun daga lokacinda dakarun Habsaha suka kori mayakan islama daga birnin akalla mutane 40,000 suka tserewa tashe tashen hankula daga Mogadishu.

A halinda ake ciki kuma gwamnatin wucin gadi ta Somalia ta umurci gidan TV na aljazeera da wasu gidajen rediyo 2 masu zaman kansu dasu dakatar da yada labari daga kasar.

Kakakin gwamnati Hussein Muahammad Mahmoud yace gwamnati ta umurci wadannan kafofin yada labari dasu dakatar da aiyukan su ba tare da bata lokaci ko kuma a tilasta maus yin hakan.

Gwamnatin dai tana zargin wadannan kafofin yada labaru da laifin keta kaidojin yada labarai ta yada labaran karya game da abubuwan da suke faruwa a Somalia,amma bata baiyana ainihin wadane dokokin ne suka keta ba.