Majalisar Dinkin Duniya tace Iran tayi mata alkawarin bayanai game da shirinta na nukiliya | Labarai | DW | 14.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya tace Iran tayi mata alkawarin bayanai game da shirinta na nukiliya

Kasar Sin,ta sake nanata cewa tattaunawa ce kadai hanyar da zaa bullowa kiki kaka game da batun nukiliya tsakanin yammacin duniya da kasashen Iran da Koriya ta arewa.

Mataimakin ministan harkokin wajen Sin Yang Jiechi ya fadawa manema labarai cewa kasarsa tayi imanin tattaunawar itace kadai hanya,ya kuma baiyana cewa,shugaba Hu Jintao zai tattauna game da wadannan batutuwa tare da Bush a lokacin ziyararsa zuwa Amurkan mako mai zuwa.

A jiya alhamis ne shugaban hukumar kula da yaduwar nukiliya Muhammad el Baradei yace kasar Iran ta baiyana masa aniyarta ta bada bayanai game da shirinta na nukiliya,sai dai Iran din tayi watsi da batun dakatar da inganta sinadaren uraniyum don anfaninta a cikin gida.

A nata bangare kuma,Koriya ta arewa tace mai yiwuwa ne ta kara inganta mata nukiliya,muddin dai taron kasashe 6 da kasar Sin zata karbi bakuncinsa ya ci tura,kodayake Koriya ta arewan tace zata koma teburin muhawara idan kasar Amurka ta saki kadarorinta data rike.