Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da shirin bude iyakokin Kashmir | Labarai | DW | 30.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da shirin bude iyakokin Kashmir

MDD ta yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Indiya da Pakistan wadda ta tanadi bude kan iyakokinsu na yankin Kashmir. Bude hanyoyi guda biyar akan iyakokin dai zai ba da damar kai dauki ga wadanda suka shiga halin lahaula sakamakon mummunar girgizar kasar da ta auku a yankin a ranar 8 ga wannan wata na oktoba. A lokacin wata ziyara da ya kai Pakistan wakilin MDD Yan Vandemoortele ya bayyana yarjejeniyar da cewa wata shawara ce mai fa´ida. Alkalumman dai sun ce mutane kimanin dubu 80 suka rasu sakamakon wannan girgizar kasa da ta auku a bangaren Pakistan na yankin Kashmir.