Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da gayyatar kai ziyara sansanin Guantanamo | Labarai | DW | 29.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da gayyatar kai ziyara sansanin Guantanamo

MDD ta tabbatar da gayyatar da Amirka ta yiwa wasu ´yan kare hakkin bil Adama masu zaman kansu zuwa sansaninta na Guantanamo inda ta ke tsare da mutanen da ta ke zargi da aikata ta´addanci. Kakakin hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD dake birnin Geneva Jose Diaz ya tabbatar da wannan gayyata wadda ta zo shekaru 4 bayan da MDD ta fara neman izinin gudanar da bincike a kurkukun, inda ake zargin sojan Amirka da cin zarafin firsinoni. A halin da ake ciki firsinoni kimanin 24 ke yajin cin abinci a sansanin na Guatanamo. Kakakin ya ce a ranar litinin mai zuwa jami´ai 3 na MDD zasu ba da sanarwa game da ranar da zasu kai ziyarar ta ganewa ido a sansanin na Guatanamo dake kasar Cuba.