1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sasantawa a Burundi

Suleiman BabayoJuly 24, 2015

Yayin da ake jiran sakamakon zaben Burundi akwai yuwuwar kasar ta fuskanci takunkumi daga kasashen duniya saboda yadda Shugaba Pierre Nkurunziza ya ki mutunta kundin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/1G42t
Burundi Wahlen Wahlstation Wähler Wahlurne
Hoto: DW/S. Schlindwein

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira a kafa gwamnatin hadin kan kasa a Burundi. A cikin wata sanarwa Sakatare Janar na majalisar Ban Ki-moon ya nemi duk wanda ya lashe zaben ya kafa gwamnati da za ta kunshi daukacin bangarorin jama'a.

A wannan Jumma'a ake sa ran hukumar zabe za ta bayyana sakamako. Jiga-jigan 'yan adawa sun janye daga zaben saboda Shugaba Pierre Nkurunziza ya taka kundin tsarin mulki wajen neman wa'adi na uku. Manyan kasashen duniya da suka hada da Amirka ta kungiyar Tarayyar Turai sun ce zaben ba shi da sahihanci. Tarayyar Turai ta ce tana shirye ta kakaba wa kasar takunkumi, yayin da Amirka take sake duba dangantaka da kasar.