1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manzon Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Sahara.

Mahmoud Ibrahim KwariJanuary 12, 2009

Sakataren majalisar dinkin duniya Mr Ban-Ki Moon ya nada tsohon Jakadan Amurka a Kasar Aljeriya Christopher Ross, a matsayin manzon musamman a yankin yammacin Saharar Afrika

https://p.dw.com/p/GWuQ
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon.Hoto: AP

Wata sanarwa daga Hedkwatar majalisar ta dinkin duniya dake Birnin New York na Kasar Amurka tace, Mr Christopher Ross zai maye gurbin Peter Van Walsum wanda wa´adin aikinsa ya kare a shekarar data gabata.

Sanarawar tayi bayanin cewa, Mr Ross zai yi aiki ne bisa kudirin majalisar mai lamba 18 13 (2008) da-ma sauran kudirce-kudircen da suka gabace shi, wadanda suka tanadi sasanta kace nacen dake tsakanin Marocco da ´Yan gwagwarmayar Sahrawi masu neman ´yancin yakin Sahrawi. Ta hanyar amfani da hikimomin siyasa, diplomasiyya da kuma mutunta´yancin al´umar yankin domin samun dawwamaman zaman lafiya.

Kafin nada shi wannann mukami Mr Christopher Ross tsohon ma´aikacin ma´aikatar harkokin wajen Amurka ne, inda yayi aikin Diplomasiyya game da harkokin yankin tsakiya, gabashi da kuma arewacin Afrika, kana ya kasance manzon Amurka na musamman a majalisar dinkin duniya kan sha´anin rikice-rikice a lardin Arewaci da gabas da kuma tsakiyar Afrika.

Tuni dai Kungiyar Polisariyo wadda tun ba yanzu ba ke gwagwarmayar neman 'yacin cin gashin kan yankin yammacin Sahara daga Marocco kuma take samun goyon bayan Kasar Aljeriya, tayi marhabin da nada Mr Ross a matsayin manzon majalisar dinkin duniya na musamman a yankin, tare da fatan cewa, zai taimaka wajen ´yantar da yankin kamar yadda yake kunshe cikin kudirin majalisar.

To amma masu lura da yadda al´amura ke tafiya a yankin, na ganin nasarar da Mr Ross zai cimma a wannan fannin kalilan ce, bisa la´akari da tsamin dangantaka dake tsakanin kasashen Marocco da Aljeriya tun a shekarar 1975, bayan da Aljeriyan ta mara baya ga ´yan kungiyar Polisariyo masu fafutukar neman ´yancin yankin Sahrawi, inda ta kai ga ta taimaka musu sun yaki dakarun Marocco.

A shekarar 1991dai majalisar dinkin duniya ta shiga tsakani ta hanyar zartar da wani kudiri dake bukatar jefa kuri´ar raba garadama, amma a wancan lokacin dukkanin bangarorin suka ki amincewa da hakan.

A watan Afrilun da ya wuce ne, Mr Peter Walsum mutumin da Mr Ross ya gada ya fusatar da ´yan kungiyar Polisariyo, a lokacin da yake gabatar da rahoto a gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda yace, batun bada ´yancin mulkin kai ga yankin Sahrawi abu ne mai wuyar tabbata, saboda Marocco ba zata yarda ta sarayar da yankin ba.

Wasu daga cikin masu lura da yadda ala´amura ke tafiya a yankin na bayyana fatan cewa, za´a iya warware rikicin ne kawai muddin Amurka da Marocco da Aljeriya suka cimma matsaya guda.

Duk da cewa, Marocco da Aljeriya da kuma kungiyar Polisariyo sunyi na´am da nadin Mr Ross a kan wannan mukami, masu sharshin al´amura a kasar Marocco na ganin cewa, zai fi karkata ne ga bangaren kungiyar Polisariyo saboda kasancewar sa tsohon Jakadan Amurka a Aljeriya.

Tun a shekarun 1970 ne dubban al´umar yankin Sahrawi da rikicin ya tarwatsa ke zaune akan duwatsu na dajin Sahara dake kasar Aljeriya kuma sun dogara ne da kayan agaji.