Majalisar Dinkin Duniya ta mika kokon bara na taimakon Timor ta gabas | Labarai | DW | 13.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta mika kokon bara na taimakon Timor ta gabas

Majalisar Dinkin Duniya tayi kira ga gaggauta taimakon Timor ta gabas,yayinda mazauna yankin suka mika kokon bararsu ga kasashen duniya.

A halin da ake ciki dai yanzu kasar Singapore tayi alkawarin baiwa yankin taimakon kudi dala 50,000 kamar yadda maaikatar harkokin wajen kasar ta sanar a yau talata.

Sanarwar tace wannan yunkuri ya biyo bayan kira da Majalisar dinkin duniya tayi ne na taimakawa jamaar yankin a jiya litinin.

A jiya ne dai majalisar ta bude asusun neman taimako ga Timor ta gabas na dalar Amurka miliyan 18 da dubu dari tara ga jamaarta 133,000 da suka tagaiyara.