1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta kara wa´adin aikinta a Iraki da shekara guda

August 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bun6

Kwamitin sulhu na MDD ya kara wa´adin aikin jami´an MDD a Iraqi da shekara daya. Dukkan kasashe membobin kwamitin sulhun sun jefa kuri´ar amincewa da kudurin tsawaita wa´adin ba tare da wata hamayya ba. Kudurin ya yi tanadin cewa ya kamata MDD ta taka muhimmiyar rawa wajen marawa shirin shimfida sahihiyar demukiradiya a Iraqi baya. Majalisar dai na da ma´aikata kimanin 400 a Iraqi daukacin su a babban birnin kasar Bagadaza.