1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta janye maaikatanta daga wasu sansanonin ta a Ivory Coast

January 19, 2006
https://p.dw.com/p/BvBh

Majalisar Dinkin Duniya,ta kwashe dukkan maaikatanta daga sansanin sojin dake Guilo a kasar Ivory Coast,biyowa bayan tashe tashen hankula na magoya bayan shugaba Laurent Gbagbo na kasar ta Ivory Coast.

Tuni dai shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya garzaya zuwa kasar a jiya laraba domin shiga tsakani a kokarinsa na ceto shirin zaman lafiya na kasar dake neman rugujewa.

Tun ranar litinin ne magoya bayan shugaban kasar ta Ivory Coast suka fara zanga zangar nuna kin amincewarsu da shawara da masu shiga tsakani na kasa da kasa sukayi, na rushe majalisar dokin kasar wadda magoya bayan Laurent Gbagbo suka fi yawa cikinta.

Bisa martani dai jamiyar dake mulki ta janye daga gwamnatin rikon kwaryar da kuma tataunawar zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya,tana mai kira da janyewar dakaru 10,000 da suka hada dana Majalisar da kuma kasar Faransa dake aiyukan wanzar da zaman lafiya a kasar.