Majalisar Dinkin Duniya ta ce za a bukaci biliyoyin dola wajen yakan murar tsuntsaye. | Labarai | DW | 12.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta ce za a bukaci biliyoyin dola wajen yakan murar tsuntsaye.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, wato WHO a takaice, ta ce barkewar murar tsuntsaye a kasar Turkiyya, wata barazana ce da za ta iya yaduwa zuwa sauran kasashen da ke makwabtaka da ita. Hukumar ta ba da wannan sanarwar ne a daidai lokacin da kasashen Turai masu makwabtaka da Turkiyyan suka tsananta matakan binciken kayayyakin abinci da ke shigowa daga ketare.

Jami’an tsaron iyaka a nan Jamus sun tsaurara nasu matakan binciken, kuma ministan kare muhalli na tarayya Horst Seehofer, ya ce mai yiwuwa gwamnati ta ba da wani sabon umarni na rufe kaji da sauran tsuntsayen kiwo a cikin akurkinsu.