Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa Njar taimako | Labarai | DW | 20.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa Njar taimako

ƙasahen duniya da ƙungiyoyi na ci-gaba da taimakawa Nijar domin yaƙi da matsalar yuwan da ke adabar ƙasar

default

  Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa ƙasar Nijar taimakon Dala Amurka biliyan 15 ƙwatakwacin sama da miliyar bakwai na kuɗin CFA domin yaƙi da matsalar yuwan da ta ke adabar ƙasar a sakamakon farin da ta  ke fama da shi.

Maljalisar dai ta ce kusan miliyon bakwai na al'umar abinda ke zaman rabi ga yawan al'umar   ƙasar baki ɗaya  na cikin wanin hali na ƙarancin cimakka.

Sanan a tsakanin shekara ta 2009 dakuma  wannan shekarar 2010 yawan yara ƙanƙana da ke kamuwa da tamowa ya ƙaru daga kashi 12 zuwa 16 inda a kowane sati yara kamar dubu shidda ne ake karɓa a cibiyoyin bada agaji na yaran.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita       : Abdullahi Tanko Bala