Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kasafin kudinta na shekaru biyu masu zuwa | Labarai | DW | 24.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kasafin kudinta na shekaru biyu masu zuwa

Dukkan kasashe 191 membobin MDD sun amince da kasafin kudin majalisar na shekaru biyu masu zuwa. Bayan muhawwara na tsawon makonni da dama, MDD ta amince ta kashe adadin kudi dala miliyan 950 wato kwatankwacin euro miliyan 801 a badi. Jakadan Amirka a MDD John Bolton ya bayyana kasafin kudin da cewa wata nasara ce ga Amirka. A halin yanzu wani kwamitin babbar mashawartar MDD dake kula da kasafin kudi ya kira taron gaggawa don ya amince da yarjejeniyar. Da zarar kwamitin ya kammala wannan aiki, membobi 191 na babbar mashawartar zasu yi wani taro don amincewa da jerin kudurori game da kasafin kudin.