Majalisar Dinkin Dunia ta nuna damuwa a game da rikici tsakanin Habasha da Eritrea | Labarai | DW | 03.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Dunia ta nuna damuwa a game da rikici tsakanin Habasha da Eritrea

Majalisar Dinkin Dunia ta nuna damuwa a game da yiwuwar sake barkewar yaki tsakanin kasashe Habasha da Erytrea.

Sakataran majalisar Koffi Annan ya bayyana samun cikkakun labarai masu nuna shirye shiryen da kasashen 2 ke yi na komawa fagen daga, bayan yarjejeniyar zaman lahia da su ka cimma, bisa jagorancin Majalisar dinkin Dunia a shekara ta 2000.

A game da haka Annan ,ya jaddada kira ga hukumomin kasashen 2 da su yi anfani da wannan yarjenejiya , ta hanyar kawce kasashen su da al´ummomin su, daga wani saban yaki.

Bayan shekaru 2 na yake yake tsakanin su, mutane kimanin dubu 80, su ka rasa rayuka a shekarun baya.

Koffi Annan ya yi kira ga hukumomin Majalisar, da su yi iya kokarin su don ganin Habasha da Eryitrea sun tabatar da zaman lahia tsakanin su.

Shugaban komitin sulhu na Majalisar dinkin dunia, ya bayyana cewa, a yanzu haka komitin na cikin tantana a kan wannan batu, tare da wakilan kasashen, don samun hanyoyin amincewar su da iyakokin da kurraru su ka shata tsakanin su, tun shekara ta 2002.