Majalisar Dinki Dunia ta maida wa gwamnatin Erythrea martani
December 8, 2005Talla
Majalisar Dinkin Dunia ta maida martani ga wa´adin kwanaki 10, da gwamnatin Erythrea ya baiwa wasu daga jami´an ta, na su fita daga kasar.
Wannan umurni ya shafi jami´an soja, da kuma na fara hulla dake zaune a Asmara babban birnin kasar ,domin sa iddo a kannyarjejeniyar zaman lahia ,da aka cimma, tsakanin Erythrea da Ethiopia, a shekara ta 2000, bayan sun share shekaru 2 su na gwabzawa.
Kakakin sakatare Jannar na Majalisar Dinki Dunia, ya hurta cewa ko da mafarki, wannan jami´ai ba za su fita ba daga Erythrea, ya kuma yi kira ga gwamnati, da ta janye wannan umurni cikin gaggawa.