Majalisar dattijan Italiya na kada kuri´ar amincewa da gwamnatin Prodi | Labarai | DW | 19.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dattijan Italiya na kada kuri´ar amincewa da gwamnatin Prodi

A yau majalisar dattijan Italiya ke kada kuri´ar amincewa da sabuwar gwamnati karkashin sabon FM Romano Prodi. Ana yiwa wannan kuri´ar kallon zakaran gwajin dafin sabuwar gwamnatin Prodi ta masu matsakaicin ra´ayin sauyi. Mista Prodi ya yi kira ga ´yan majalisar dattijan da su marawa gwamnatinsa baya, kwana daya bayan ya bayyana shirye shiryen sa wadanda suka hada da janye dakarun Italiya daga Iraqi tare da bullo da sahihan matakan farfado da tattalin arzikin kasar. Prodi ya ce gwamnatin sa kwakkwara ce duk da cewa rinjayen kujeru biyu kadai ta samu a zaben da aka gudanar cikin watan da ya gabata.