1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dattijan Amurka ta bada sahalewa ga dokar tuhumar masu laifin taáddanci

September 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bui1

Majalisar dattijan Amurka ta amince da daftarin ƙudiri da shugaba George W Bush ya gabatar mata wanda zai bada damar daukar tsauraran matakai a tuhumar mutanen da ake zargi da ayyauakn taáddanci. Shugaba Bush ya buƙaci Tun da farko majalisar wakilai ta ƙasar ta rattaba amincewa da daftarin dokar wadda ake sa ran shugaba Bush zai sanyawa hannu nan bada jimawa ba. Bush ya baiyana amincewa da daftarin da majalisar dattijan ta yi da cewa wata manuniniya cewa Amurka zata yi amfani da dukkan ƙarfin iko wajen farautar makiyan ƙasar domin hana aukuwar harin taáddanci a kan Amurka